(ABNA24.com) A gobe Asabar 11 ga watan Afrilu ne za’a fara amfani da sabon tsarin yaki da cutar Corona a nan birnin Tehran, a dai-dai lokacinda kashi 2/3 na ma’aikata a birnin zasu koma kan ayyukansu a yayinsa. Sannan sauran kashi 1/3 kuma zasu yi aiki daga nesa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shafin yanar gizo na magajin garin birnin Tehran, Golam-Riza Abbas Pasha ya na fadar haka a yau Jamma’a.
Labarin ya kara da cewa a cikin sabon tsarin yakar cutar ta Corona dai, za’a dauki matakan binciken ma’aikata a dukkan ma’aikatun gwamnati da kuma na masu zaman kansu, don tabbatar da cewa ba wanda yake dauke da alamun cutar Covid 19 da zai shiga ya yi aiki tare da wadanda basa dauke da alamun cutar.
Banda haka za’a dauki dukkan matakan tsabta na daddaiku mutane da kuma gaba daya, wadanda suka hada da amfani da magungunan kashe kwayoyin cutar a dukkan ma’aikatu da kuma kamfanoni da kasuwannin da sauransu.
Pasha, ya kara da cewa ma’aikata zasu rika zuwa aiki daga karfe 7-02 na rana, daga ranakun Asabar-Laraba, sannan daga karfe 7.30-01 na rana a ranakun Alhamis har zuwa abinda hali yayi.
/129
11 Afirilu 2020 - 05:13
Lambar labari: 1024267
A gobe Asabar 11 ga watan Afrilu ne za’a fara amfani da sabon tsarin yaki da cutar Corona a nan birnin Tehran, a dai-dai lokacinda kashi 2/3 na ma’aikata a birnin zasu koma kan ayyukansu a yayinsa. Sannan sauran kashi 1/3 kuma zasu yi aiki daga nesa.